Bugu da kari, shugaba Xi ya ba da umurnin daukar matakan gano wadanda suka bace tare da kashe wutar da ta tashi sanadiyar fashewar.
A nasa bangare firaminista Li ya lashi takwabin ganin an gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin hadarin da ya faru.
Yanzu haka dai majalisar gudanarwar kasar ta Sin ta aike da wata tawagar bincike karkashin jagorancin ministan kula da harkokin tsaron jama'a Guo Shengkun don jagorantar aikin ceton gaggawa a wurin da hadarin ya faru
Masu aikin ceto dai sun bayyana cewa, mutane 17 ne suka mutu kana sama da 400 suka jikkata sanadiyar fashewar da ta faru a ranar Laraba da dare a wani dakin ajiye kayayyaki a birnin na Tianjin mai tashar jiragen ruwa.(Ibrahim)