in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar Guangming ta fitar da sharhi game da rawar da Sin ta taka a yakin kin Fascist
2015-08-06 11:20:43 cri

Jaridar Guangming ta fidda wani sharhi da Hu Dekun ya rubuta, mai taken "Bayani game da rawar da Sin ta taka a yakin nuna kiyayya ga Fascist na duniya".

A yayin yakin, kasar Sin tana daya daga cikin kasashe hudu mafiya kokarin dakile 'yan Fascist a duniya. Fagen daga na kasar Sin ya zama muhimmin fili a nahiyar Asiya, kana yana daya daga cikin manyan filayen yakin nuna kiyayya ga 'yan Fascist na duniya.

A sakamakon yakin cacar baki, a cikin shekaru 70 bayan yakin nuna kiyayya ga Fascist, kasashen yammacin duniya sun yi watsi, tare da rashin nuna girmamawa ga muhimmin matsayi da muhimmiyar rawar da Sin ta taka a yakin, matakin da sharhin ya nuna cewa ko kadan ba adalci a cikin sa.

Sharhin ya ce da farko Sin ita ce kasa ta farko da ta nuna kiyayya ga harin Fascist a duniya, wadda ta bude filin yakin nuna kiyayya ga Fascist na farko.

Kana Sin ta dakile harin da sojojin kasar Japan suka kai, kuma filin yaki na kasar Sin ya zamo muhimmin fili na yaki a nahiyar Asiya. Abu na uku, yakin da Sin ta yi ya dakatar da harin neman mallakar duniya da Japan ta yi kokarin aiwatarwa, wanda ya taimakawa kasashen Soviet Union da Amurka da Britaniya da sauran kasashen kawancenta.

Na hudu, Sin ta yi kokarin sa kaimi ga kafa kawancen yaki da Fascist na duniya, da shiga ayyukan sake kafa odar duniya bayan yakin.

Tarihi ya shaida cewa, babu shakka Sin, da Amurka, da Britaniya da Soviet Union, sun kasance kasashe hudu mafiya girma a duniya na yaki da Fascist.

Abu ne dai mai wuya a samu nasarar wanzar da ci gaba bayan yakin duniya na biyu, don haka ya kamata Sin da kasashen duniya su dauki alhakin dake kan su, don kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa, da hadin gwiwa a duniya a halin yanzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China