A jiya ne shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya bude babban ginin cibiyar kasuwanci mai suna M. PEACE da kamfanin gine-gine na kasar Sin (CCECC) dake Rwanda ya gina.
A cikin jawabinsa shugaba Kagame ya yaba matuka da ingancin ginin da kuma yadda kamfanin ya kammala aikin cikin sauri, ya kuma bayyana cewa, cibiyar kasuwancin za ta taka muhimmiyar rawa bayan da aka fara amfani da ita.
Bugu da kari, shugaba Paul Kagame ya yi kira ga jami'an da ke kula da aikin raya ababen more rayuwa da su yi namijin kokarinsu wajen samar da yanayin da ya dace ga masu sha'awar zuba jari a kasar Rwanda, ta yadda hakan zai taimaka wajen bunkasa birnin Kigali, fadar mulkin kasar.
Shugaban reshen kamfanin CCECC dake kasar Rwanda Wang Lei ya yi bayani da cewa, fadin cibiyar kasuwancin ta M. PEACE mai hawa 17 ya kai murabba'in mita dubu 42, sannan akwai wuraren cin abinci da nishadi da yin sayayya da ofisoshi da kuma gidaje, kuma wannan shi ne gini mafi girma a kasar ta Rwanda.(Lami)