in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na nuna shakku kan matakin Faransa na sake fito da takardun kisan kare dangi
2015-04-09 11:04:25 cri

'Yan kasar Rwanda sun bayyana shakkunsu kan matakin da kasar Faransa ta dauka na maido da takardun da ke da nasaba da kisan kare dangi na shekarar 1994 a kasar Rwanda kan tebur, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da miliyan daya.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya sanar a ranar Talatar da ta gabata wani shirin ba da dama ga samun saukin kai ga takardun da suka shafi wannan lamari ga kowa, tare da bayyana cewa. yanzu wadannan takardu ba za su kancewa wani abin sirri ba, a cewar wata majiya mai tushe ta kusa da fadar shugaban kasar Faransa a gaban manema labarai a ranar Talata.

Takardun na shekarar 1990 zuwa shekarar 1994 sun kunshe bayanan sakamakon tarukan da aka yi bisa sirrin tsaro, da kuma wasu takardun na masu ba da shawara ga shugaban kasar Faransa na lokacin, Francois Mitterand, da ke da nasaba da kisan kare dangi a cikin wannan karamar kasa dake tsakiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China