Mutanen kasar Rwanda sun fara bikin tunawa da kisan kare dangi na shekarar 1994 karo na 21 a ranar Talata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da miliyan daya, ta hanyar shirya da bukukuwa iri daban daban, da suka hada da ajiye furanni a dandamalin tunawa da mamatan, gabatar da wani tubali ga sauran gawawwakin da aka gano, gabatar da bayanan shaidu, gudanar da taruruka, da kunna kendir.
Wadannan bukukuwa za su gudana har tsawon mako daya, amma bikin tunawar zai kai har zuwa ranar 4 ga watan Yuli, dake nuna kwanaki 100 na kisan kiyashin.
Bikin tunawa na wannan shekera ya kasance bisa taken "Tunawa, ilimantarwa da kariya", da kara mai da hankalin jama'ar kasar da gamayyar kasa da kasa kan batun mammunan sakamakon kisan kiyashi da tuna baya.
Ministar wasannin motsa jiki da al'adu ta kasar Rwanda, madam Julienne Uwacu, ta bayyana cewa, bukukuwan wannan shekara za su gudana a kauyuka domin tattauna shirin wakarwa, hadin kai da sasantawa tsakanin al'ummar kasar Rwanda.
A cewar madam Uwacu, mummunan sakamakon kisan kiyashi na kasancewa babban kalubale a cikin gida, har yanzu mutane na ci gaba da gudanar da dangantaka ta karya da nuna banbanci game da kisan kiyashin shekarar 1994. (Maman Ada)