Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, ya soki kasashen yammacin duniya da tilasta nuna karfinsu da nuna isa da kai kan kasashen Afrika da ke kokarin sake gina kansu.
Korafe korafen shugaba Kagame sun biyo bayan cafke shugaban hukumar leken asirin kasarsa, mista Karenzi Karake a ranar Asabar, wadanda jami'an Burtaniya suka kama bisa doka.
Shugaban kasar Rwanda ya yi wannan furuci ne a yayin da yake jagorantar bikin rantsar da sabon mininistan ilimi, da wasu sabbin 'yan majalisu hudu da kuma sabbin alkalai, bikin da aka gudanar a zauren majalisar dokokin kasar ta Rwanda. (Maman Ada)