in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta shigo da zakuna na musamman daga Afirka ta Kudu
2015-07-27 09:17:42 cri

Mahukuntan kasar Rwanda sun sanar da cewa, yanzu dai sun saki nau'in zakuna nan na musamman guda 7 da ta sayo daga kasar Afirka ta Kudu cikin gandun dajin Akagera na musamman da aka gina mai fadin murabba'in kadada 1,000 da ke kasar.

Bayanai na nuna cewa, da farko dai kasar ta Rwanda ta shigo da zakunan ne a kokarin da kasar ke yi na bunkasa bangaren yawon shakatawarta, sashen da shi ne ke samarwa kasar kudaden shiga mafi tsoka.

Babban manajan gandun dajin na Akagera Jes Gruner ya shaida wa manema labarai cewa, gandayen dajin Afirka tare da hadin gwiwar hukumar raya kasa ta Rwanda ne suka yi aikin shigo da wadannan zakuna daga kasar Afirka ta Kudu zuwa kasar ta Rwanda.

Yanzu haka dai Zakukan sun fara sabawa da yanayin gandun dajin kasar, kuma har sun fara neman abinci da kansu, bayan killace su na wani lokaci kafin su saba da canjin da suka tsinci kansu ciki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China