Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta shaidawa taron manema labarai a yau cewa, kasar Sin da ragowar kasashen da ke yankin Asiya da kuma duniya baki daya, suna jiran irin jawaban da shugabannin na Japan za su yi a game da wannan biki. Ta ce, kasar Sin tana bukatar Japan da ta amince da irin ta'asar da sojojin suka aikata.
Bayanai na nuna cewa, galibin kasashen da ke yankin Asiya na nuna damuwa cewa, Abe na iya gurbata gafarar da tsohon firaministan kasar Tomiichi Murayama ya yi a mukumance a shekarar 1995 a jawabin da zai yi. (Ibrahim)