Yayin ganawar shugaba Xi ya shaidawa Abe cewa, kasar Sin tana fatan bangaren Japan zai ci gaba da bin hanyar tabbatar da zaman lafiya da rungumar manufofin tsaro da na soja da suka dace.
Shugaba Xi ya ce, kasancewar kasashen biyu makwabtan juna, hadin gwiwar samun bunkasuwa mai kyau tsakanin kasashen biyu ya dace da muradun al'ummomin kasashen da kuma duniya baki daya.
Ya kuma bukaci kasar ta Japan da ta kara nuna abubuwa masu sahihanci a zahiri da za su taimaka wajen karfafa amincewa tsakanin kasashen biyu da kuma sauran kasashen da ke makwabtaka da ita, sannan ta taka rawar da ta dace wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar baki daya.
A nasa jawabin firaminista Abe ya ce, Japan a shirye ta ke ta bi turbar bunkasuwa cikin lumana, sannan gwamnatin kasar mai ci za ta ci gaba da bin manufofin gwamnatocin kasar da suka gabata dangane da tarihi.
Ya kuma bayyana cewa, Japan a shirye ta ke ta aiwatar da abubuwan nan hudu da Sin da Japan suka cimma yarjejeniya a kai, kula da batutuwan da ke da nasaba da hakan ta yadda za su kasance mafarin inganta hadin gwiwar manyan tsare-tsare da samun moriyar juna tsakanin sassan biyu.(Ibrahim)