in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu wani babban ci gaba ba wajen neman jirgin sama nan da ya bace
2014-03-10 16:11:20 cri

Jirgin sama mai lamba MH370, wanda ya tashi daga Kuala Lumpur, babban birnin kasar Malaysia da misalin karfe 1 da minti 20 na safe na ranar 8 ga wata, amma kawo ya zuwa yanzu ya bace a kan hanyarsa zuwa Beijing, har zuwa tsakiyar ranar 10 ga wata, ba a samu shi ba. Bangarorin da abin ya shafa sun zafafa karfin nemansa tare da zaburar da kaimi wajen nemensa, amma ba a samu babban ci gaba ba tukuna.

Bisa labarin da muka samu, an ce, Sin ta riga ta tura jiregan ruwa guda 9 wanda tuni suka isa inda aka rasa tumtubar jirgin sama don gudanar da aikin ceto. Ban da wannan kuma, wani jirgin 'yan kasuwa na Sin da wani jirgin ruwa na 'yan sandan Sin sun riga sun isa tekun da aka shakkar rasa tumtubar MH370, tare da sauran jiragen ruwa 3 suna zuwan wurin don gudanar da aikin ceto.

Shugaban kasar Malaysia Tuanku Abdul Halim Muadzam Shah ya yi jawabi na tafiyar da harkokin siyasa a ran 10 ga wata a majalisar dokoki cewa, shi da uwar gidansa da jama'ar duk kasar sun mai da hankali kan lamarin bacewar jirgin Malaysia mai lamba MH370. Ya kara da cewa, ya nuna tausayi ga dukkan fasinjoji, da ma'aikatan jirgin, da dangoginsu, kuma yana fatan dukkan 'yan uwan fasinjoji da ma'aikata za su nuna juriya da karfin zuciya a gabashin batun.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China