in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja ta yi bikin murnar bikin gargajiya na Duanwu na kasar Sin
2015-06-20 15:38:08 cri


Gabannin bikin gargajiya na kasar Sin wato Duanwu, cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, tare da hukumar raya al'adun gargajiya ta Abuja sun shirya wasannin raye-raye da kade-kade domin murnar wannan biki na kasar Sin cikin hadin-gwiwa.

 

Bikin Duanwu bikin gargajiya ne na Sinawa, wanda ke da dogon tarihi na tsawon shekaru kimanin dubu biyu. A kan yi wannan biki ne a ranar 5 ga watan Mayu na kowace shekara, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ana kuma kiran bikin da sunaye iri iri, misali, bikin Duanyang, bikin watan Mayu, bikin mawaka, bikin wasan kwale-kwale da sauransu.

Wani babban dalilin da ya sa al'ummar kasar Sin ke wannan biki na Duanwu shi ne, domin tunawa da marigayi Qu Yuan, da kuma irin ra'ayinsa na kishin kasa, kuma muna iya gano haka ne idan mun yi bincike a kan al'adu da dama da ake bi na yin bikin, ciki har da tseren kwalekwale, da cin wani nau'in abincin da ake kira Zongzi da sauransu.

Wasan tseren kwalekwale wata muhimmiyar al'ada ce ta bikin Duanwu. Akwai wata tatsuniya game da dalilin da ya sa ake wannan wasa a yayin bikin Duanwa, wadda ta nuna cewa, bayan da Qu Yuan ya tsunduma cikin kogi, al'ummar daular Chu sun yi bakin ciki kwarai, wasu ma sun je har tafkin Dongting da kwalekwale don su ceto shi, amma, kokarinsu ya bi ruwa. Daga nan, a kan shirya wasan tseren kwalekwale a kowace ranar 5 ga watan Mayu bisa kalandar gargajiyar kasar Sin domin tunawa da marigayin. Ana ganin tseren da ake yi zai taimaka wajen korar kifayen da ke cikin kogin domin kada su cinye gawar Qu Yuan. Lubabatu, ko ba haka ba.

Ban da wasan tseren kwale-kwale, cin Zongzi a bikin Duanwu wata al'ada ce ta daban ta jama'ar kasar Sin. Zongzi wani irin nau'in abinci ne da ake hadawa, ta hanyar kunshe shinkafa cikin ganye, wanda ke da dogon tarihi tare da nau'o'i da yawa. Amma ba wai an kirkiro Zongzi ne saboda tunawa da marigayi Qu Yuan ba ne, a'a, a game da asalinsa, in an yi bincike, za a tara ra'ayoyi da yawa. Akwai wani daga cikinsu da ya fi samun karbuwa, an ce, kafin shekaru dubu dari biyar, lokacin da aka fara yin amfani da wuta domin dafa abinci, a kan kunshe shinkafa da ganye a kuma kona shi a cikin wuta, bayan ya dafu sai a cire ganyen a ci, ko da yake, irin wannan abinci ba Zongzi ba ne, amma ana ganin shi ne asalin Zongzi. Amma a game da dalilin da ya sa al'ummar Sinawa ke cin Zongzi a yayin bikin Duanwu shi ne, domin an ce, bayan da Qu Yuan ya tsumduma cikin kogi, sai jama'a suka jefa Zongzi cikin kogi, domin fatan kifaye za su ci Zongzi a maimakon gawarsa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China