Shugaban kungiyar Emmanuel Onourah wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai a birni Lagos, cibiyar harkokin kasuwancin kasar ya ce, muddin majalisar dokokin kasar ba ta hanzarta sanya hannu kan dokar da ta shafi bangaren man kasar ba, hakan na iya barazana ga jarin da za a zuba a wannan bangaren daga sherkarar 2015 zuwa 2020 adadin ya kai kusan dala biliyan 80.
Shugaban kungiyar ya kara bayyana cewa,rashin sanya hannu kan wannan doka na iya rage yawan kudaden shigar da gwamnatin kasar ke samu a bangaren man da ya kai dala biliyan 44 cikin wannan lokaci.(Ibrahim)