Ban da Seif al-Islam Qaddafi, wadanda aka yankewa hukuncin kisan sun hada da tsohon firaministan kasar Al-Baghdadi Ali Al-Mahmoudi, da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Abdullah al-Sanoussi da sauransu.
Seif al-Islam Qaddafi dai bai bayyana a zaman kotun ba. Sai dai ya saurari hukuncin da kotun ta yanke masa ta yanar gizo. Ana dai tsare da Seif al-Islam a Zintan dake da tazarar kilomita 150 daga birnin Tripoli a kudu maso yammacin kasar, tun cikin shekarar 2011 ya zuwa wannan lokaci da aka yanke masa hukuncin kisa.
Sakamakon mamaye birnin Tripoli da kungiyar masu ra'ayin addini ta Fajr Libya ta yi a watan Agustan bara, tare da kafa gwamnatin ceton kasa, ya tilastawa gwamnatin wucin gadin Libiyan kaura zuwa gabashin kasar. A kuma wannan lokaci ta yi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da wannan hukunci wanda ta ce an yanke shi ba bisa ka'ida ba.
A jiya Litinin ma'aikatar kula da harkokin shari'a ta gwamnatin wucin gadi a Libiyan ta fidda wata sanarwa wadda ke cewa hukuncin da wannan kotu za ta yanke ya sabawa doka. Kuma alkalin zai yanke hukuncin ne ala tilas karkashin matsin lamba. (Fatima)