Yau Asabar 18 ga wata, ake gudanar da bukukuwan karamar sallah a jihar Xinjiang ta Sin.
A wannan rana, Mista Abdulla Litip wanda ke zauna a kusa da masallacin Erdaoqiao na birnin Urumqi da ke jihar Xinjiang ta kasar Sin, yana cikin farin ciki sosai. Abdulla Citip wanda ke da shekaru 69 a duniya yana sallolinsa biyar a kowace rana. Ya ce, a lokacin zafi aka yi azumin watan Ramadan na tsawon kwanaki 30, tunda aka kawo karshen azumin dole ne a yi murnar bikin karamar sallah. A wannan rana, matasa su kan je gaida tsofaffi tare da basu kyauta, haka ma irin wannan al'ada na gudana tsakanin makwabta.(Fatima)