Da safiyar wannan rana, a birnin Xining, hedkwatar lardin Qinghai, musulmai 'yan kabilu daban daban da ke bin addinin musulunci sun tashi zuwa masallacin Dongguan, kuma mutanen da ke zuwa sallah sun cika makil a titin da ke kewayen masallacin da ke da tsawon kilomita 5. Da misalin karfe 9 na ranar, babban limamin masallancin ya jagoranci sallar Idi a gaban musulmai sama da dubu 100.
Haka su ma musulmai kimanin dubu 180 na kabilun Hui da Dongxiang da Baoan da Sala da Kazak dake lardin Gansu suka yi bikin karamar Sallah a wannan rana.
A lardin Ningxia kuma, a masallacin Najiahu dake da tarihi na shekaru fiye da 500, musulmai sun yi sallhar karshe na cikin watan Ramadan bisa jagorancin Liman. (Fatima)