Sai dai kuma Bankin ya yi bayanin cewa tafiyar hawainiya da tattalin arzikin kasar na Sin ke yi zai rika faruwa ne sannu a hankali ba wai an kai karshen mataki ne da zai fadi kasa ba, kamar yadda Sudhir Shetty, babban jami'in bankin a kan tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific. Ya yi bayanin wanda ya ce tafiyar hawainiya na ci gaban tattalin arzikin Sin ba zai ba da wani tasiri a sauran kasashe ba.
Har ila yau ya yi nuni da cewar idan kasar Sin ta fuskanci faduwa kai tsaye wanda da wuya hakan ya faru lallai zai shafi yankuna masu samar da ababen bukatar yau da kullum kamar masu safarar karafa na Mongoliya da masu safarar kwal na Indonesia matuka.
Dangane da yadda Sin take a bayanin duniya, an bayyana cewar kwaskwarimar a bangarori kamar na masana'antu da samar da hidima zai taimaka wajen ragen radadin da matakan da aka dauka za su kawo domin ci gaba da kula da basusukan kananan hukumomi da kuma bankunan da ba su da wani kuzarin a zo a gani.
A kuma bangaren kasuwannin gine-gine, Bankin ya ce babban gyara a wannan fanni game da farashin gidaje a kasar zai kasance a hakan duk da cewar za'a fuskanci matsin lamba a kan farashin a gundumomin da ba su ci gaba cikin sauri ba. (Fatimah Jibril)