in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwazon Sin a fagen gudanar da sauye-sauye kyakkyawan misali ne, in ji shugaban bankin duniya
2013-10-11 09:35:23 cri

Shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim, ya bayyana kwazon da kasar Sin ke nunawa a fagen samar da sauye-sauyen tattalin arziki, a matsayin wani kyakkyawan misali ga kasashe masu samun bunkasuwa, da ma ragowar kasashen masu tasowa.

Kim, wanda ya yi wannan tsokaci yayin wani taron manema labarai, gabanin bude taron shekara shekara, da babban bankin da hadin gwiwar takwaransa na IMF ke gudanarwa, ya ce, duk da halin da ake ciki na koma bayan ci gaba a fannin bunkasuwa, kasar Sin na kara dagewa wajen gudanar da sauyi mai ma'ana.

Bugu da kari Kim, ya yaba kokarin da kasar ta Sin ke yi na habaka fannin ba da hidima da cinikayyar cikin gida, ya kuma bayyana yankin cinikayya cikin 'yanci dake Shanghai, a matsayin tsarin da ke dada samun tagomashi, duk kuwa da tafiyar wahainiyar da ake samu a fannin bunkasuwar tattalin arzkin kasar a halin yanzu. A cewarsa, daukar wadannan matakai ya dace da burin da ake da shi yanzu haka, na wanzar da managartan sauye-sauyen da suka dace. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China