in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An damke wasu mutane 4 da ake zaton 'yan fashin teku a Najeriya
2013-12-09 10:02:14 cri

Dakarun sojan ruwan Najeriya, sun sanar a ranar Lahadi cewa, an kama 'yan fashin teku 4 a jihar Rivers da ke kudancin kasar bisa zargin keta matakan tsaron jiragen ruwa a mashigin ruwan kasar da ke yammacin Afirka.

Wata sanarwa da kakakin sojan ruwan kasar, Laftana kwamanda Abdulsalam Sani ya bayar a birnin Fatakwal, ya bayyana cewa, dakarun sojan ruwan ne suka kama wadanda ake zargin yayin sintirin da suka saba gudanarwa.

Sai dai binciken wucin gadi na bayyana cewa, wadanda ake zargin na da hannu a abubuwa da aka aikata na keta wadannan matakan tsaro, wadanda suka kawo koma baya ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Kakakin ya ce, tuni aka mika wadanda ake zargin ga hannun 'yan sandan shiyya da ke tsibirin Bonny don kara gudanar da bincike tare da hukunta su.

Bayanai na nuna cewa, a 'yan shekarun nan, ana kara fuskantar ayyukan fashin teku da fashi da makami a yankin tekun Guinea mai arzikin mai, lamarin da ke haifar da damuwa matuka ga kasashen duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China