in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsawaita wa'adin yaki da 'yan fashin tekun Somaliya
2013-11-19 10:18:03 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana amincewa da tsawaita wa'adin aikin yaki da 'yan fashin teku a kasar Somaliya da shekara daya, yana mai kira da daukacin kasashen duniya, da hukumomin shiyya-shiyya, da su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin an magance wannan matsala tun daga tushe.

Kwamitin wanda ya bayyana yankunan tekun kasar ta Somaliya a matsayin mafi hadari a dukkanin fadin duniya, ya kuma bayyana ayyukan 'yan fashin tekun a matsayin barazana ga ma'aikatan sufurin ruwa, da ma tattalin arzikin yankin baki daya.

Don gane da irin matakan da suka wajaba a dauka domin shawo kan wannan matsala, kwamitin tsaron na MDD ya ayyana samar da sojojin ruwa domin aikin sintiri, da amfani da jiragen sama domin samar da tsaro, tare da kwace jiragen ruwa, da kayan aiki da irin wadannan bata gari ke amfani da su, a matsayin wasu daga hanyoyin da suka dace a bi, domin shawo kan wannan matsala.

Haka zalika kwamitin ya jaddada kudurinsa, na hada kai da ragowar kasashen dake yankin, wajen kafa wata kotun musamman, da za ta rika hukunta laifuka masu alaka da fashin teku a kasar ta Somaliya, da ma sauran kasashe dake wannan yanki na gabashin Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China