Gwamnonin manyan bankuna na kasashen Afrika, galibi daga gabashi da kudancin nahiyar za su hadu domin tattauna asusun mallaka da za'a kafa domin daidaita tattalin arzikin nahiyar.
Bankin Reserve na Zimbabwe, John Mangudya zai bude taron da za'a yi a kasar Switzerland a ranar Asabar din nan mai zuwa 27 ga wata, a cewar masu shirya taron wato MEFNI wadda ke da rassa a kasashe 14 na Afrika.
Babban darektan cibiyar ta MEFNI Caleb Fundanga a ranar Laraban nan ya ce, an dade ana zargin nahiyar ta Afrika da rashin amfani da albarkatun, ta yadda za a samar da ci gaba mai dorewa da kuma sauyi mai ma'ana a kan tattalin arziki. Kuma asusun mallaka na daya daga cikin abubuwan da ake ganin za su taimaka don cimma hakan.
Shi dai asusun mallaka wani zuba jari ne da kasashen za su rika yi a ainihin kaddarorin na kudade, hannayen jari, harkokin gidaje, karafa masu daraja, ko kuma akasin hakan kamar asusun ajiya na musamman, da kuma asusun ajiya na manyan masana'antun hadin gwiwwa masu zaman kansu.
Tattaunawar za ta biyo bayan binciken da wata cibiyar kasa da kasa a kan harkokin bankuna da kula da kaddarori Invetecs cikin hadin gwiwwa da cibiyar ci gaban kasa da kasa ta CID suka gudanar tare da cibiyar Belfer a jami'ar Harvard. (Fatimah)