Wannan ita ce ganawar shugabannin biyu cikin watanni biyu da suka gaba kadai. Na farko ita ce tattaunawar da suka yi a ranar 8 ga watan Mayu a birnin Moscow kafin su gana da sauran shugabannin da suka halarci bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin kare kai da Rashan ke kira yakin duniya na biyu.
A watan Satumba ne kuma ake sa ran shugaba Putin na Rasha zai kawo ziyara nan kasar Sin don halartar bikin cika shekaru 70 da nasarar kawo karshen yakin kin jinin harin Japanawa da zai gudana a nan birnin Beijing. (Ibrahim)