in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya nanata burin kasarsa na wanzar da zaman lafiya
2015-07-08 10:22:24 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake nanata burin kasarsa, game da ci gaba da bunkasa zaman lafiya, ko da yake a cewar sa hakan ba zai sanya a manta da tarihin abubuwan da suka faru a baya ba.

Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin ziyarar da ya kai wurin adana kayan tarihi, game da yakin kin jinin harin Japanawa wanda ake kira "Marco Polo Bridge", a shirye-shiryen da ake yi na bikin cika shekaru 70, da cimma nasarar dakile mamayar da sojojin Japan suka yiwa al'ummar Sinawa.

Mr. Xi ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da martaba matakan wanzar da zaman lafiya, cikin yanayi na taka-cancan game da makomarta a nan gaba. Kaza lika kasar na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, na ganin an tabbatar da zaman lafiya a duniya, a hannu guda kuma za ta ci gaba da bin tsarin mulki irin na gurguzu mai yanayin musamman da ya dace da kasar.

An dai baje hotuna 1,170 game da yakin kin jinin harin Japanawa, da kuma kayayyakin nune-nune 2,834 a wajen baje kolin dake kusa da gadar Lugou, wurin da dakarun kasar ta Japan suka kaddamar da cikkaken farmaki kan kasar Sin shekaru 78 da suka gabata.

Ana fatan gudanar da cikakken biki game da wannan batu, da ma nasarar kawo karshen yakin duniya na 2 a ranar 3 ga watan Satumbar dake tafe a nan birnin Beijing, inda za a gudanar da macin soji na musamman. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China