Hakan dai na kunshe ne ciki wani rahoto da bankin na duniya ya fitar a Talatar nan. Rahoton ya kara da cewa a baya Sinawa masu zuba jari na maida hankali ne ga fannin ma'adanai da gine-gine, amma a yanzu hakan na sauyawa, inda nahiyar kasar ke kara yawan jarin ta a fannin sarrafa kayayyaki daga masana'antu.
Rahoton ya ce daukar matakan samar da managarcin yanayin zuba jari, zai baiwa Afirka karin damar cin gajiya daga dinbin jarin da take samu.
Babban bankin duniya ya fitar da wannan rahoto ne yayin wani taro kan harkar zuba jari a Afirka , wanda bankin, da kasar Sin da kuma kasar Habasha suka yi hadin gwiwar shiryawa a birnin Addis Ababa.