Kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin ko CRBC a takaice da ke aikin gina sabon layin dogo a kasar Kenya, ya kaddamar da wata cibiyar horas da fasahohi a garin Voi da ke gabar teku.
Manufar kafa wannan cibiya ita ce, horas da ma'aikatan da ba su da kwarewa, dabarun aiki na zamani, da kuma wadanda da ma ke aikin shimfida layin dogon sabbin hanyoyin tafiyar da aiki.
A jawabinsa yayin bikin kaddamar da shirin mataimakin manajan da ke kula da aikin Han Feng ya ce, cibiyar tamkar wata matattarar hazikai ce ga kamfanin na CRBC da kuma kasar ta Kenya. Kuma ana sa ran kara bullo da irin wadannan cibiyoyi a sauran wuraren da kamfanin ke gudanar da irin wadannan ayyuka.
Sama da injiniyoyi da masu sana'o'in hannu 200 a kasar Kenya ne za su fara amfana da kashin farko na shirin na tsawon watanni uku.(Ibrahim)