in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aikin gina cibiyar nazari ta Sin da Afrika a Nairobi
2014-12-05 15:27:42 cri

Bisa tsarin karfafa huldar hadin gwiwar kimiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ne, za'a kafa wata cibiyar nazari ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a birnin Nairobi, a jami'ar noma da kimiyya ta Jomo Kenyatta, tare da tallafin gwamnatin kasar Sin.

A ranar Alhamis, mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto, da mai kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya, Tian Lin, da kuma mataimakin darekta janar na cibiyar dangantakar kasa da kasa ta cibiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, Qiu Huansheng sun halarci bikin kaddamar da ayyukan gina wannan cibiyar bincike ta hadin gwiwa, irinta ta farko da kuma za ta kunshe wani lambun itatuwa bisa fadin kadada 40.

A cikin jawabinsa, mista Ruto ya nuna yabo kan dangantakar Sin da Afrika a fannin kimiyya da fasaha da ma kirkire kirkiren zamani domin gaggauta sauye sauyen tattalin arziki da na jama'a a nahiyar.

Haka kuma mista Ruto, ya tabbatar da cewa, kasar Kenya za ta kasance wani dandali a fannin bincike da fasahohin zamani tare da taimakon kasar Sin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China