in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Sin sun kaddamar da sabon shirin baiwa gandun daji kariya
2014-07-03 09:54:06 cri

Mahukuntan kasashen Kenya da Sin sun kaddamar da wani sabon tsari, da zai taimaka wajen kare albarkatun gandun daji daga duk wata nau'in barazana.

Makasudun shirin na gwaji dai shi ne baiwa al'ummun dake zaune kusa da gandayen daji tallafin inganta rayuwa, ta yadda za su samu zarafin kulawa da albarkatun dazuzzuka, da kare rayukan namun daji, musamman a yankunan gabashin Afirka.

Da yake karin haske game da shirin, babban daraktan hukumar KWS mai lura da gandun daji a kasar ta Kenya Mr. Erustus Kanga, ya ce, ana fatan sabon shirin zai rage matsin lamba da gandayen daji, da dazuzzuka ke fuskanta, tare da dakile mummunar sana'ar nan ta haramtacciyar farauta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China