in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da musayar yawu game da zargin da ake yiwa Afirka ta Kudu na ba da cin hanci
2015-06-01 13:33:33 cri
A jiya Lahadi wasu bayanai sun kara fitowa dake nuna ga zargin da ma'aikatar shari'ar kasar Amurka ke yiwa kasar Afirka ta Kudu na amfani da dalar Amurka miliyan 10, a matsayin toshiyar baki domin samun kuri'un wasu masu ruwa da tsaki, lokacin da kasar ke neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010, zargin da gwamnatin Afirka ta Kudun, da hukumomin wasannin motsa jikin kasar suka dade suna musuntawa.

Wasu kafofin watsa labarun kasar dai sun fidda wata wasikar sirri, wadda ta tabbatar da cewa, Afirka ta Kudun ta aikata wannan laifi da ake zargin ta da aikatawa.

Jaridar "The Sunday Times" ta kasar Afirka ta Kudun ta fitar da wani dogon bayani, inda ta ce, ta samu wata wasika da hukumar wasan kwallon kafa ta kasar ta rubuta ga hedkwatar FIFA. Inda a cikin ta aka tabbatar cewa, Afirka ta Kudun ta amince FIFA, ta yi amfani da dalar Amurka miliyan 10, a matsayin toshiyar baki ga hukumomin wasan kwallon kafa na kasashen dake yankunan arewaci da tsakiyar Amurka, da Carribean, kudin da bisa doka FIFA za ta baiwa Afirka ta Kudun, domin daukar nauyin gudanar da gasar ta cin kofin duniya.

An ce, takardar mai dauke da kwanan wata na watan Maris, shekara ta 2008, na kuma dauke da sa hannun shugaban hukumar wasan kwallon kafar na lokacin Moller fee Oliphant. Bisa bincike an gano cewa, sau uku ana fidda kudade daga tsarin ajiya ko biyan kudi na hukumar FIFA, zuwa asusun wasu hukumomin wasan kwallon kafa dake yankunan arewaci da tsakiyar Amurka, da Carribean.

A wani ci gaban kuma shugaban hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu Danny Jordan, ya amince da cewa, ko da yake kasarsu ta taba mika kudi dalar Amurka miliyan 10 a shekarar 2008, a cewar sa kudaden ba wai an yi amfani da su ne a matsayin toshiyar baki ba. Ya ce, an yi amfani da kudin ne wajen tallafawa bunkasar hukumomin wasan kwallon kafa dake yankunan arewaci da tsakiyar Amurka, da Carribean. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China