in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta nanata bukatar gudanar da tattaunawa wajen warware rikicin Burundi
2015-06-29 09:48:14 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) ta nanata bukatar da ake akwai ta gudanar da tattaunawa da cimma daidaito don lalubo bakin zaren warware rikicin kasar Burundi.

Shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU Madam Nkosazana Dlamini Zuma wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta kuma bayyana takaicin kungiyar game da mummunan yanayin siyasa da tsaron da ake ciki a kasar.

Shugabar ta kuma jaddada cewa, yanayin siyasar da ake ciki a kasar na iya rusa duk wani ci gaban da aka samu bayan kammala yarjejeniyar zaman lafiya da sassantawa da aka cimma a Arusha a shekarar 2000, da kuma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekara 2003. Ta ce, hakan na iya yin illa ga zaman lafiya da tsaro a kasar Burundi, har ma da shiyyar baki daya.

Bugu da kari, Madam Zuma ta tabo batun shawarar da aka cimma a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2015, yayin taron kolin kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC) a birnin Dar-es-Salaam na kasar Tanzaniya, da kuma taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU (PSC) da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a ranar 13 ga watan Yunin shekarar 2015, wadanda suka zayyana matakan magance rikincin kasar cikin lumana.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China