in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na adawa da duk wani abin da zai janyo tashin hankali a Burundi
2015-03-27 09:44:09 cri

Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika (AU), Dlamini-Zuma da ke ziyarar aiki a kasar Burundi, ta bayyana cewa, kungiyar tarayyar Afrika na adawa da duk abin da zai iyar gurgunta zaman lafiya da janyo baraka a cikin kasar a wannan lokaci, inda 'yan kasar Burundi ke shirin gudanar da zabuka a cikin watan Yuni mai zuwa.

Fatanmu shi ne kasar Burundi ta tsaya bisa turbar zaman lafiya da lumana domin fuskantar kalubaloli daban daban da take fama da su, musammun ma na ilimi, ababen more rayuwa, makamashi da sauransu, in ji madam Dlamini Zuma a gaban manema labarai.

Babbar jami'ar ta jaddada cewa, game da sauran kasashen Afrika goma sha bakwai da ke shirin gudanar da zabuka a shekaru masu zuwa, Burundi kasa ce da ke daukar hankalin kungiyar AU sosai domin ita kasa ce ta yi fama da manyan wahalhalu irin daban daban.

Nahiyar Afrika na son hada kai tare da 'yan kasar Burundi domin taimaka musu wajen kokarin warware matsalolinsu, in ji jami'ar.

Ziyarar madam Dlamini Zum, ta zo daidai lokacin da jam'iyyun adawa suke allahwadai da baiwa matasan dake goyon bayan gwamnatin kasar makamai, kana kuma shugabannin kawacen adawa na barazanar korar mambobin hukumar zabe mai zaman kanta (CENI) da suke zargi da shirin aikata magudi a yayin wadannan zabuka domin tallafawa jam'iyyar dake mulki.

A yayin da ita kuma jam'iyyar dake mulki, CNDD-FDD take zargin 'yan adawa da neman yin zagon kasa ga zabuka ta hanyar ayyukan tashe tashen hankali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China