in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kiran a gudanar da tattaunawa a Burundi
2015-05-18 09:36:28 cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta nanata muhimmancin gaggauta yin tattaunawa da sasantawa a kasar Burundi.

Shugabar hukumar zartaswar kungiyar Madam Nkosazana Dlamini Zuma wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa ta kara da cewa, tana sa ido kan abubuwan da ke wakana a Burundi.

Madam Zuma ta kuma yi kira ga gwamnatin Burundi da sauran masu ruwa da tsaki, da su yi kokarin samo bakin zaren warware wannan matsala a siyasance don fitar da kasar daga matsalar da ta ke fuskanta.

Ta ce, hanya daya tilo ta warware wannan matsala, ita ce yin tattaunawa ta yadda za a kiyaye muhimman nasarorin da aka cimma tun lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da sulhuntawa game da rikicin Burundi a Arusha a shekarar 2000, ta yadda za a karfafa tsarin demokiradiya da martaba doka da samar da yanayin da ya dace na gudanar da zabe cikin lumana, gaskiya da adalci.

Daga nan ta kuma nanata kiraye-kirayen da AU da EAC suka yi ga mahukuntan Burundu da su dage zaben kasar da aka yi shirin gudanarwa.

Madam Zuma ta nanata kudurin kungiyar AU na ci gaba da ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da kuma ganin an shimfida tsarin demokiradiya a kasar ta Burundi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China