in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta shawarci tattaunawa a Burundi
2015-05-15 10:21:04 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta jaddada bukatar dake akwai ta tattaunawa don cimma matsaya a kasar Burundi, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa a cibiyar kungiyar dake birnin Adis Ababa na kasar Habasha a ranar Laraba wadda ta tabbatar da cewa, shugaban kwamitin kungiyar Madam Nkosazana Dlamini Zuma za ta ci gaba da lura da abin da ke wakana a kasar.

Haka kuma dangane da hakan ne shugaban kwamitin kungiyar ta halarci taron musamman na kasashen gabashin nahiyar Afrika da aka yi a ranar Laraba a birnin Dares Salam na kasar Tanzaniya, kamar yadda sanarwa ta bayyana.

A wajen taron, Madam Dlamini Zuma ta tunatar da ka'idojin kungiyar na kin amincewa da duk wani sauyin gwamnati da kundin tsarin mulkin kasa bai amince da shi ba, da kuma cikakkaen goyon bayanta na bin doka da tsarin demokradiya, kamar yadda yake a cikin dokokin kungiyar da tsarin zabe da kuma mulki.

A don haka shugaban kwamitin kungiyar ta AU ta yi suka da kakkausar murya ga yunkurin juyin mulkin da aka yi a Bujumbura na kasar ta Burundi, san nan ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su kauce wa duk wani nau'in yanayi da ka iya dagula halin da ake ciki tare da kiyaye tada hankula da ka iya kaiwa ga lalata kayayyaki da asarar rayuka ko saka al'umma rasa matsugunnansu.

Madam Nkosazana Dlamini Zuma ta jaddada goyon bayan kungiyarta AU a duk wani shiri da shugabannin kasashen gabashin Afrikan suke yi, musamman ma matakan da aka amince da su a taron Dares Salam.

Haka kuma shugaban kwamitin kungiyar ta AU ta sake ba da tabbacinta na ci gaba da aiki tare da kungiyar kasashen gabashin Afrikan, da ma sauran masu ruwa da tsaki na kasa da kasa domin ba da gudunmuwa da za'a cimma zaman lafiya da mafita mai karko a cikin matsalar ta Burundin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China