Wani jigo a jam'iyyar Fatah ta Falasdinawa Azzam El-Ahmed, ya ce, ana daf da komawa teburin shawarwari, tsakanin wakilan Isra'ila da na Falasdinu, game da 'yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sassan biyu da kasar Masar ke tallafawa.
El-Ahmed ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa, za a dora game da shawarwarin da ake yi ne nan da tsakiyar watan Nuwambar dake tafe.
Kafin hakan dai an sanya ranar Litinin din nan a matsayin ranar da za a ci gaba da zaman tattaunawa tsakanin sassan masu ruwa da tsakin, sai dai harin da aka kai kan wasu dakarun sojin kasar Masar a birnin Sinai, ya tilasa dage zaman.
A ranar 26 ga watan Agustan da ya shude ne dai Masar ta shiga tsakani, wajen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, matakin da ya kawo karshen dauki ba dadin da sojojin Isra'ila da mayakan kungiyar Hamas suka shafe kwanaki 50 suna yi. Wanda kuma ya haddasa kisan Falasdinawa 2,450, tare da raunata wasu 11,100. (Saminu)