in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu bukatar nuna damuwa game da tsaron shugaba al-Bashir, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sudan
2015-06-15 20:39:25 cri
Shugaban kasar Sudan Omer Hassan Al-Bashir, na ci gaba da halartar taron shugabannin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta (AU) a kasar Afirka ta Kudu, kuma babu wata bukata ta nuna damuwa dame da tsaron shugaban, a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan,.

A jiya Lahadi, shugaba Al-Bashir ya halarci taron koli na kungiyar ta AU da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, a kuma gabar da wata babbar kotu dake zaman ta a birnin Pretori ta bada umurnin hana shi fita daga kasar bisa wani wa'adi na wucin gadi.

Tun dai bayan fitar wannan labari ne hankula ke ta komawa kan wannan batu a kasar Sudan da ma sauran sassan kasashen Larabawa. Game da hakan, ministan harkokin wajen kasar Sudan Kamal Ismail ya bayyana cewa, yanzu haka labaran da kafofin yada labarai ke bayarwa don gane da bacewa, ko tsare shugaba Al-Bashir, dukkansu ba su da tushe bare makama, kuma ba su da alaka da ainihin yanayin da shugaba Al-Bashir ke ciki a kasar Afirka ta Kudu.

An dai yi imani cewa Afirka ta Kudu za ta cika alkawarinta na maraba da zuwan shugaba Al-Bashir. Kuma a cewar ministan yanzu haka ana gudanar da harkokin taron na AU yadda ya kamata. Babu kuma wata barazana game da tsaron shugaban kasar ta Sudan. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China