in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Al-Bashir ya kafa sabuwar majalissar ministoci tare da 'yan sauye-sauye
2015-06-07 13:18:47 cri
Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya gudanar da sauye-sauye ga sabuwar majalissar zartaswar da ya kaddamar, 'yan kwanaki bayan da lashe babban zaben kasar da ya gudana watan Afirilu.

Cikin ministocin da shugaban na Sudan ya sauyewa wuraren aiki akwai Ibrahim Ghandour, wanda ya koma ma'aikatar harkokin wajen, sai Mohammed Zayed da zai rike ma'aikatar albarkatun mai, yayin da kuma laftana janar Mostafa Osman Abeed, ya zamo mukaddashin ministan tsaron kasar.

Kaza lika an tabbatar da Bakri Saleh, da Hassabo Mohammed Abdul-Rahman a mukamansu na mataimaka ga shugaba Al-Bashir.

A ranar Talatar makon da ya kare ne shugaban na Sudan ya ci layar kama aiki, a matsayin zababben shugaban kasar Sudan a sabon zangon shekaru 5, yana mai alkawarta gudanar da mulki cikin adalci da kare kimar kasa, tare da martaba kundin mulkin kasar yadda ya kamata.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa shugaba Al-Bashir ya lashe zaben da ya gabata da gagarumin rinjaye, duk kuwa da kiraye-kirayen da 'yan adawa daga jihohin Blue Nile, da South Kordofan da Darfur suka rika yi, na a kauracewa zaben. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China