A jiya ne hanyar jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,344 da kamfanin CRCC na kasar Sin ya gina a kasar Angola ta fara aiki.
Hanyar wadda za ta hade birnin Lobito da ke bakin ruwa a yammacin kasar da garin Luau da ke kan iyakar kasar, shi ne layin dogo mafi girma na biyu da kamfanin ya gina a Afirka, baya ga layin da ya hade Tanzaniya da Zambia wanda aka gina a shekarun 1970.
Hanyar jirgin kasan da aka gina tun a shekarar 2004, yanzu haka za ta hadu da layin da ya hade Angola da Zambiya da kuma layin da ake fatan ginawa a nan gaba da zai hade kasashen Tanzaniya da Zambia. (Ibrahim)