Mahukuntan kasar Kenya sun fara wata tattunawa da kamfanin kasar Sin wanda ke ginin layin dogo na zamani a kasar, da nufin duba yiwuwar tsawaita nisansa zuwa garin Naivasha dake arewa maso yammacin kasar.
Shugaba Uhuru Kenyatta ne ya bayyana hakan, jim kadan da kammala ziyararsa a wurin da ake gudanar da aikin a yankin Voi. Ya ce, idan har an cimma matsaya game da tsawaita layin dogon, za a kara kusan kilomita 120 bisa asalin kwangilar da aka daddale, ya zuwa rukunin masana'antu da za a gina a Naivasha, wurin da ake fata samar da wutar lantarki ta zafin kasa.
Wannan sabon layin dogo da za a gina a Kenya dai zai hade manyan biranen kasar, wato Nairobi zuwa Monbasa, shi ne kuma aiki irin sa mafi girma da ake gudanarwa a kasar, tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1964.
Kaza lika aikin zai hade Kenya da kasashen gabashin Afirka, kamar Tanzania, da Uganda, da Rwanda, da Burundi da kuma Sudan ta Kudu. (Saminu)