Gwamnatin Senegal ta kaddamar a ranar Laraba, a birnin Dakar da shirin kafa wani asusu bisa tsarin shiri'ar musulunci wato Sukuk domin tattara Sefa biliyan 100, ta yadda za'a samar da kudaden zuba jari, in ji wata majiya mai tushe.
Shirin da aka ma taken "Sukuk na kashi 6,25 cikin 100 na Senegal na shekarar 2014 zuwa 2018" wata gidauniyar hadin gwiwa ce ta ba da rancen kudi (FCTC) da ake kan hanyar kafawa, bisa tunanin hadin gwiwar bankin raya yammacin Afirka BOAD da bankin musuluncin kasar Senegal (BIS).
Makasudin yin haka ga gwamnatin Senegal shi ne don tattara Sefa biliyan 100 daga wajen masu zuba jarin dake sha'awar samun hannun jari dake zuwa daidai da kokokin da suka shafi harkar kudi bisa tsarin musulunci. (Maman Ada)