A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Angola José Eduardo dos Santos, inda shugabannin 2 suka yaba wa hadin gwiwar sada zumunta dake tsakanin kasashen 2, sun kuma amince su hada kai wajen zurfafa huldar abokantaka a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni, a kokarin kara kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri.
A yayin shawarwarin, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin na son hada kai da Angola cikin kwamitin sulhu da sauran hukumomin duniya, da inganta tuntubar juna da hadin gwiwa kan ajandar ayyukan raya kasa bayan shekarar 2015, sauyin yanayi, wanzar da zaman lafiya da bunkasuwa a Afirka da dai sauransu, a kokarin kiyaye moriyar dukkan kasashe masu tasowa. Kana kasar Sin na son hada kai da kasashen Afirka ciki had da Angola wajen raya Sin da Afirka tare, a kokarin ganin jama'ar Sin da Afirka sun ci gajiyar dankon zumuncin da ke tsakanin bangarorin 2.
Firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma ya gana da shugaban na Angola a wannan rana. (Tasallah Yuan)