Shugaban kasar Chadi Idriss Deby da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari da a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar ta Chadi, sun yi alkawarin yin aiki tare don yakar kungiyar nan ta Boko Haram.
Shugaban na Chadi ya kuma yaba kokarin shugaba Buhari na Najeriya na ganin bayan kungiyar ta Boko Haram, inda ya bayyana kudurinsa na hada kai da Najeriya a wannan gwagwarmaya.
Shugaba Deby ya ce, ya zama wajibi rundunar hadin gwiwar da aka kafa ta fara aiki don maido da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya da dukkan yankunan da mayakan Boko Haram suka lalata.
Bugu da kari, shugabannin biyu sun kuma bukaci kasashen duniya da su taimakawa hukumar raya kasashen da ke yankin tafkin Chadi (LCBC) da sauran kasashen da ke makwabtaka da su.
A ranar 25 ga watan Mayu ne kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin zaman lafiya da tsaro Ismail Chergui ya kaddamar da rundunar hadin gwiwa ta hukumar raya tafkin chadi da za ta yaki kungiyar Boko Haram. (Ibrahim)