Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta mayar da cibiyarta ta kaddamar da hare-hare, da yaki da kungiyar Boko Haram zuwa birnin Maidugurin jihar Borno tun daga ranar Litinin.
Wata sanarwa da mukaddashin kakakin rundunar kanar Sani Usman ya sanyawa hannu, ta ce, hakan ya biyo bayan umarnin da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayar, cikin jawabinsa na rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu.
Sanarwar ta kara da cewa, cibiyar wadda za ta rika karbar umarni daga manyan hafsoshin sojin kasar, za ta zamo hanyar fadada ayyukan da ake yi na yaki da ta'addanci da ayyukan masu tada kayar baya.
Sai dai sanarwar ta ce, tsare-tsaren ayyukan cibiyar wadda aka yiwa lakabi da "Zaman Lafiya", ba zai sauya matakan da ake dauka ba, illa dai kawai za a shigar da sabbin dabarun fuskantar mayakan kungiyar ta Boko Haram. Har wa yau an kafa wata cibiyar ta daban a birnin Yola, fadar mulkin jihar Adamawa.
Jihohin Adamawa, da Borno da Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, su ne suka fi fuskantar yawan hare-hare daga mayakan Boko Haram. Kuma bisa kiyasi ayyukan kungiyar sun sabbaba kisan sama da mutane 13,000, tsakanin shekarar 2009 zuwa 2015. (Saminu)