in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Togo da Benin sun kawo goyon baya ga Nijar kan yaki da Boko Haram
2015-02-26 10:22:52 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya tarbi a ranar Talata a filin jirgin saman kasa da kasa na Diori Hamani dake Niamey, shugaban kasar Togo Faure Yassingbe Eyadema, da na kasar Benin Thomas Boni Yayi.

Shugabannin biyu sun je ne da sunan takwarorinsu na Afrika, domin kawo goyon bayan al'ummomin kasashensu biyu ga shugaban kasar Nijar da jama'arsa, kan yaki da kungiyar Boko Haram.

Bayan wata ganawa a fadar shugaba Mahamadou Issoufou, shugabannin uku sun shirya wani taron manema labarai. Da yake magana a gaban 'yan jarida, shugaban Togo Faure Eyadema ya sake jaddada goyon bayan kasashensu biyu ga kasar Nijar da al'ummarta, tare da nuna juyayi ga mutanen da hare haren ta'addanci a jihar Diffa suka rutsa da su, da kuma jajantawa iyalansu.

Haka kuma, shugabannin biyu sun nuna yabo sosai ga yadda al'ummar kasar Nijar ta zama tsintsiya madaurinki daya a yayin taron gangamin nuna goyon baya ga jami'an tsaron kasar na FDS a ranar 17 ga watan Febrairun shekarar 2015.

A yanzu, Boko Haram barazana ce ga shiyyar, wajibi shiyyar ta dauki matakan murkushe ta, in ji shugaban kasar Togo.

A nasa bangare, shugaban kasar Benin Boni Yayi ya bayyana cewa, mu al'umma guda ne dake cikin shiyya guda, abin da ya shafi Nijar, ya shafe mu. Matsalar Boko Haram, ta kasance babbar matsala da ta wuce iyakokin Nijeriya har ta kawo ga daya daga cikin makwabtanmu, wato kasar Nijar ke nan, al'ummomin kasashenmu biyu suna tare da kasar Nijar, in ji shugaba Boni Yayi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China