in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun hallaka wani jami'in tsaro a Nigeriya
2015-06-08 10:32:21 cri

Wassu da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun hallaka wani jami'in tsaro a Ungwan Keke a jihar Kaduna dake arewacin Nigeriya bayan wata musayar wuta da suka yi a ranar Lahadin nan da jami'an tsaro.

Yan ta'addan su biyu an ce suna zaune ne a wannan unguwa, inda jami'an tsaro suka kai samame, amma sun tsere bayan lokaci da aka dauka ana musayar wuta da su, in ji wani da abun ya faru a kan idanun shi.

Kamar yadda ganau din ya yi bayani wanda shi ma yake zaune a wannan unguwa ya kuma bukaci a sakaya sunan shi saboda yadda al'amarin yake na tsaro, ya ce, jami'an tsaron sun kawo samame ne da misalin karfe 1 na dare, kuma kana iya jin karar bindiga ta ko ina, sannan wadanda ake zargin sun tsere bayan da suka harbe daya daga cikin jami'an tsaron har lahira.

Da shi ma yake tabbatar da hakan mai unguwar Suleiman Mohammed ya ce, mazauna wajen karar bindiga ce ta tada su daga barci, yana mai bayanin cewa, jami'an tsaron da suka kawo samame na hadin gwiwwa sun hada da sojoji da jami'an liken asiri, wadanda daga baya suka bukaci mazauna da kowa ya fice daga cikin gidan shi domin kauce wa tsautsayi.

Gidan da wadanda ake zargin 'yan Boko Haram din ke zauna gaba daya a hargitsa shi, in ji wani da shi ma ya shaida hakan.

Sai dai duk kokarin da wakilinmu ya yi na kaiwa ga rundunar sojin ta Kaduna domin karin bayani, hakan bai yiwu ba har zuwa lokacin da muka samu wannan labarin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China