in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Angola yana hanyar kawo ziyarar aiki a Sin
2015-06-08 09:34:59 cri

Rahotanni daga birnin Luanda na kasar Angola na tabbatar da cewar, shugaba Jose Eduardo Dos Santo da ya tashi a jiya Lahadi yana kan hanyar shi ta kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa, ziyarar da za ta ba shi damar daidaita shiri da tsarin gwamnatin shi dangane da yanayin tattalin arziki da na hada hadar kudi da take fuskanta, tare da sake duba dangantakar hadin gwiwwa da yanzu haka take tsakanin kasashen biyu.

Sakataren harkokin wajen kasar na Angola Manuel Augusto ya shaida wa manema labarai hakan a filin jiragen saman kasa da kasa jim kadan da tashin shugaban daga Luanda.

Ya ce, ziyarar tana da muhimmancin gaske idan aka duba dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, musamman game da ci gaba da yake wakana yanzu haka, sannan wannan ziyarar ta zo a daidai lokaci mai muhimmanci na ci gaban tattalin arziki da walwalar kasarsa.

Daga cikin tawagar shugaban kasar, akwai ministan harkokin gida kuma shugaban ma'aikata na fadar gwamnati Edeltrudes Costa, ministan harkokin wajen kasar George Chikoti,, ministan sufuri Augusto Tomas, ministan ciniki Rosa Pacavira, da kuma ministan makamashi da ruwa Joao Baptista Borges. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China