in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda sun saki Sinawa da ake tsare da su a Angola
2014-12-23 09:51:16 cri

A yau ne 'yan sanda a Angola suka saki Sinawa 18 daga cikin 31 da aka tsare a kasar bayan shiga tsakanin da ofishin jakadancin Sin da ke Angola ya yi.

Wani jami'i a ofishin jakadancin kasar ta Sin da ke Angola Zhao Haihan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an saki Sinawan ne bayan da suka gabatar da cikakkun takardunsu na izinin zama a kasar.

Sai dai sakataren majalisar kungiyar 'yan kasuwan Sinawa da ke kasar Angola Zhao Hongbing ya yi korafin cewa, an gallaza wa Sinawan yayin wannan lamari.

Ya ce, galibin Sinawa da kamfanonin kasar Sin da ke kasar na zaune ne bisa doka, kuma sun bayar da gudummawa wajen sake gina kasar bayan yaki.

Da ya ke karin haske, mataimakin kwamandan 'yan sandan yankin Luanda Francisco Ribas ya ce, sun dauki wannan mataki ne da nufin kakkabe bakin haure da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba.

A ranar 19 ga watan Disamba ne 'yan sanda a kasar ta Angola suka kama bakin haure kimanin 1,000 da suka fito da kasashe daban-daban, ciki har da Sinawa sama da 300 da nufin kama bakin hauren dake zauner a kasar ba tare da izini ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China