Rahotanni daga birnin Luanda, fadar gwamnatin kasar Angola, na cewa, cibiyar kasuwancin kasar Sin dake Angolan, ta bude wani sashe na ba da tallafin kwararru a ranar Litinin.
Wannan dai sashe zai rika baiwa Sinawa 'yan kasuwa, da ma'aikata a sassa daban daban da ma, ta samun tallafin kwararrun a fannin shari'a, da kuma yadda za su rika gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Hakan dai zai karawa Sinawan dake zaune cikin kasar ta Angola, damar sanin hanyoyin yin rajistar sana'o'insu, da samun biza, da kuma hanyoyin warware matsalolin cinikayya, da dai sauran lamura masu alaka da hakan.
Yanzu haka dai kididdiga ta nuna cewa, akwai akalla Sinawa 'yan kasuwa 500 a kasar Angola, baya ga sama da kwarraru, da ma'aikatan kamfanonin gine-gine 100,000 dake gudanar da ayyukan sake ginin kasar ta Angola.
An dai yi imanin cewa, wadannan Sinawa na baiwa kasar gagarumar gudumawa, ta fuskar bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Saminu)