in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki Sinawan da ake tsare da su a Angola
2014-12-22 09:42:22 cri

Rahotanni daga ofishin jakadancin kasar Sin da ke Angola na cewa, yanzu haka an saki galibin Sinawan da 'yan sanda suka tsare ranar Jumma'a a Luanda, babban birnin kasar.

Wani jami'i a ofishin jakadancin na Sin Li Chong ya shaida wa ma'aikatun harkokin waje da cikin gida da kuma hedkwatar 'yan sandan kasar cewa, matakin da 'yan sandan suka dauka na tsare Sinawan ba tare da sun gabatar da kansu ba bai dace ba.

Shi ma babban sakataren majalisar kungiyar 'yan kasuwan Sinawa da ke Angola, Zhao Hongbing ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, galibin Sinawa da kamfanonin da ke kasar na zaune ne bisa doka, kuma sun ba da gudumawa wajen sake gina kasar bayan yaki.

A jawabinsa, mataimakin kwamandan 'yan sandan yankin Luanda Francisco Ribas ya jaddada cewa, 'yan sandan sun dauki matakin ne da nufin farautar bakin haure da ke zaune a kasar ba bisa doka ba, ba wai Sinawa kawai ba.

A ranar Jumma'a ne 'yan sanda a kasar ta Angola suka damke bakin haure kimanin 1,000 a Luanda, babban birnin kasar, ciki har da 'yan kasar Portugal da jamhuriyar demokiradiyar Congo da kuma Sinawa sama da 300 da nufin kakkabe bakin haure da ke aiki a kasar ba bisa ka'ida ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China