in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen ruwan sojin Sin sun kai ziyarar kara dankon zumunci a Angola
2014-06-06 14:09:22 cri

Rundunar sojojin ruwa kasar Sin ta 16, tare da tawagar jiragen ruwa masu yi masu rakiya sun isa tashar ruwan Luanda, a jiya Alhamis domin fara gudanar da wata ziyarar kwanaki ukku ta kara dankon abokantaka da kasar Angola, wannan ziyarar ita ce ta farko da sojojin ruwan na Sin suka taba kaiwa Angola, wacce ke Afrika.

Kwamandan rundunar ruwan Li Pengcheng ya shaidawa 'yan jarida cewar, kasar Sin da Angola sun kasance suna gudanar da hulda ta abokantaka da juna, kuma rundunonin sojojin kasashen biyu su ma suna ci gaba da gudanar da wasu ayyuka tare na kara dankon zumunci, wanda ya hada da gudanar da horon kwararru da ma'aikata, da kuma hada hannu a ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Makasudin ziyararta a Angola shi ne a kara bunkasa fahimtar juna da amincewa da juna, tare da samar da huldar aiki na rundunonin dakarun kasashen, musammam sojojin ruwan kasashen biyu.

A lokacin ziyarar, ma'aikatan jiragen ruwan tawagar kasar Sin za su yi musayar basirun kwarewa a fannin ayyukan sojojin ruwa da takwarorinsu na Angola, kuma jiragen ruwan yakin kasar Sin, wadanda aka yi wa lakabi da "Yancheng" da "Luoyang", za'a bar su bude domin ziyara daga jama'ar kasar ta Angola.

Wannan ziyara ta tawagar jiragen ruwan kasar Sin zuwa Angola, ita ce ziyara ta shidda da tawagar jiragen kasar Sin suka kai Afrika, wannan ziyarar za ta kai su kasashen Namibia da Africa ta Kudu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China