in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan za ta gayyaci kamfannonin Sin don raya harkokin sadarwa na 4G a kasar
2015-05-19 10:19:34 cri
Ministan kimiyya da fasaha, da harkokin sadarwa na kasar Sudan Tahani Abdullah, ya sanar da cewa nan da watanni 3 masu zuwa, kamfannonin sadarwa na kasar za su fara aikin fadada harkokin sadarwar na 4G a kasar.

Abdullah, ya ce mai yiwuwa ne za a gayyaci kamfannonin kasar Sin dake da kwarewa da kwazo, ciki har da kamfanin Huawei, don gudanar da wannan aiki, matakin da ake fatan zai sanya Sudan zama daya daga cikin kasashen Afrika kalilan da ke da fasahar 4G. Ministan ya fadi hakan ne a gun taron karawa juna sani, game da harkokin sadarwa da ya gudana a jiya Litinin.

Ya ce, kamar sauran kasashen Afirka har yanzu Sudan ma na sahun baya, a fannin harkokin sadarwa, kuma bunkasa wannan fanni ta hanyar gudanar da gyare-gyare a bangaren muhimman ababen more rayuwa ciki hadda fannin sadarwa, lamari ne da zai yi tsada matuka. Sabo da haka, idan aka fara amfani da fasahar Internet ta 4G kai tsaye, hakan zai yi matukar amfani ga kasar. Ko da yake ministan bai fayyace wuraren da za a fara amfani da fasahar ta 4G a farko a kasar ba.

Yanzu haka dai a manyan biranen kasar ta Sudan, ana amfani da harkokin sadarwa da manyan kamfanoni 4 suke samarwa, sai dai wannan harka ba ta da tasiri a yankunan karkara, da kauyuka, kuma farashin Internet yana da tsada kwarai a irin wadannan sassa. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China