An tattauna harkokin da ke jawo hankalin kasa da kasa a taron ministocin harkokin wajen membobin kungiyar SCO
A gun taron majalisar ministocin harkokin wajen kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Moscow, ministocin harkokin waje masu mahalartar taron sun yi musayar ra'ayoyi kan manyan batutuwan duniya da na yankuna shiyya shiyya kamar halin da ake ciki a kasar Afghanistan, halin da yammacin Asiya da arewacin Afirka da dai sauransu. Ministocin suna ganin cewa, kamata ya yi a yi shawarwari a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa bisa tushen girmama juna da dai na tsoma baki daga kasashen waje don warware matsala da kuma tabbatar da zaman lafiya mai karko. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku