Mutane 5 sun rasa rayukan su, kana wasu mutane 6 sun samu raunuka, sakamakon fashewar wasu boma-boman da aka dasa cikin wata mota, a wata tashar bincike dake birnin Misrara, birni na 3 mafi girma a kasar Libiya.
Wani jami'i da ya nemi a boye sunansa dake aiki a hukumar tsaron birnin, ya ce mutane 3 ne suka mutu nan take a harin na jiya Lahadi, sakamakon tarwatsewar da motar mai dauke da Bam din ta yi, yayin da wasu 8 suka ji raunuka, ciki hadda mutum 2 da suka samu manyan raunuka, kana daga bisani suka rasu bayan da aka garzaya da su asibiti.
Tuni dai reshen kungiyar IS dake kasar ta Libiya ya sanar da daukar alhakin kai harin ga kafofin watsa labaru.
Kafin hakan dai a ranar 5 ga watan Afrilun da ya shude ma an kaddamar da wani harin kunar bakin wake na boma-bomai, wadanda aka boye cikin wata mota, a wata tashar bincike dake gabashin birnin Misrata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, kana mutane 21 suka samu raunuka.
A wancan karo ma dai reshen kungiyar IS dake kasar ta Libiya ne ya dauki alhakin kai farmakin. (Lami)